Mark 12

Misali na ʼYan Haya

1Saʼan nan ya fara yi musu magana da misalai, ya ce, “Wani mutum ya shuka gonar inabi. Ya kewaye ta da katanga, ya haƙa rami domin matsen inabin, ya kuma gina ɗakin gadi. Sai ya ba wa waɗansu manoma hayar gonar inabin, saʼan nan ya yi tafiya. 2Da lokacin girbi ya yi, sai ya aiki wani bawa wajen ʼyan hayan, don yǎ karɓo masa ʼyaʼyan inabin daga wurinsu. 3Amma suka kama shi, suka yi masa dūka, suka kore shi hannun wofi. 4Sai ya sāke aikan wani bawa wurinsu, amma suka bugi wannan mutum a kai, suka wulaƙanta shi. 5Har yanzu ya sāke aikan wani. Wannan kuwa suka kashe. Ya aika waɗansu da yawa; suka bubbuge waɗansu, sauran kuwa suka kashe.

6“Sauran mutum ɗaya da ya rage ya aika, ɗa, da yake ƙauna. Daga ƙarshe sai ya aike shi, yana cewa, ‘Za su girmama ɗana.’

7“Amma ʼyan hayan suka ce wa juna, Aha! ‘Wannan shi ne magājin. Ku zo mu kashe shi, gādon kuma yǎ zama namu.’ 8Sai suka kama shi suka kashe, suka jefa shi bayan gonar inabin.

9“To, me, mai gonar inabin zai yi ke nan? Zai zo yǎ karkashe dukan ʼyan hayan nan, ya kuma ba wa waɗansu gonar inabin. 10Ba ku taɓa karanta wannan Nassi ba:

“ ‘Dutsen da magina suka ƙi,
shi ne kuwa ya zama dutsen kusurwan gini.
11Ubangiji ya yi wannan,
ya kuma yi kyau a idanunmu’
Zab 118.22, 23
?”

12Sai suka nemi hanyar da za su kama shi, domin sun gane ya yi misalin a kansu ne. Amma suka ji tsoron taron, sai suka bar shi suka yi tafiyarsu.

Biyan Haraji ga Kaisar

13Daga baya, sai suka tura waɗansu Farisiyawa da mutanen Hirudus zuwa wurin Yesu, domin su sa masa tarko a cikin maganarsa. 14Suka zo wurinsa suka ce, “Malam, mun san kai mutum ne mai mutunci. Ba ka bin raʼayin mutane, don ba ka nuna bambanci. Amma kana koyar da hanyar Allah bisa ga gaskiya. Daidai ne a biya wa Kaisar haraji, ko babu? 15Mu biya ko kada mu biya?”

Amma Yesu ya san munafuncinsu, sai ya yi tambaya, ya ce, “Don me kuke ƙoƙarin sa mini tarko? Ku kawo mini dinari in ga.”
16Suka kawo masa kuɗin, sai ya tambaye, su ya ce, “Hoton wane ne wannan? Kuma rubutun wane ne wannan?”

Suka ce, “Na Kaisar.”

17Sai Yesu ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku ba wa Allah kuma abin da yake na Allah.”

Suka yi mamakinsa ƙwarai.

Aure a Tashin Matattu

18Saʼan nan Sadukiyawa da suke cewa, babu tashin matattu, suka zo masa da tambaya. 19Suka ce, “Malam, Musa ya rubuta mana cewa, in ɗanʼuwan wani mutum ya mutu, ya bar mata babu ʼyaʼya, dole mutumin ya auri gwauruwar, yǎ kuma samo wa ɗanʼuwansa ʼyaʼya. 20To, an yi waɗansu ʼyanʼuwa guda bakwai. Na fari ya yi aure, ya mutu babu ʼyaʼya. 21Na biyun ya auri gwauruwar, sai shi ma ya mutu, babu ʼyaʼya. Haka kuma na ukun. 22A gaskiya, ba ko ɗaya daga cikin bakwai ɗin da ya bar ʼyaʼya. Daga ƙarshe, macen ta mutu. 23To, a tashin matattu, matar wa za ta zama, don duk su bakwai nan sun aure ta?”

24Yesu ya ce, “Ashe, ba a cikin kuskure kuke ba saboda rashin sanin Nassi, ko ikon Allah? 25Saʼad da matattu suka tashi, ba za su yi aure ba, ba kuwa za a ba da su ga aure ba. Za su zama kamar yadda malaʼiku suke a cikin sama. 26Game da tashin matattu kuwa-ashe, ba ku karanta a cikin littafin Musa ba, game da labarin ɗan kurmin nan mai cin wuta da Musa ya gani a jeji, yadda Allah ya yi magana da shi, ya ce, ‘Ni ne Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub’
Fit 3.6
?
27Shi ba Allah na matattu ba ne, sai dai na masu rai. Kun yi mummunan kuskure!”

Dokar da Ta fi Girma Duka

28Wani daga cikin malaman dokoki ya zo ya ji suna muhawwara. Da ya lura cewa Yesu ya amsa musu daidai, sai ya tambaye shi, ya ce, “A cikin dukan dokoki, wacce ta fi girma duka?”

29Yesu ya ce, “Wadda ta fi girma duka, ita ce wannan: ‘Ya ku Israʼila, ku saurara, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne. 30Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan hankalinka, da kuma dukan ƙarfinka.’
M Sh 6.4, 5
31Na biyun ita ce, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’
L Fir 19.18
Ba wata doka da ta fi waɗannan.”

32Mutumin ya ce, “Malam, ka faɗi daidai. Daidai ne da ka ce, Allah ɗaya ne, babu kuma wani sai shi. 33Nuna ƙauna ga Allah da dukan zuciyarka, da dukan ganewarka, da dukan ƙarfinka, da kuma nuna ƙauna ga maƙwabcinka kamar kanka, ya fi dukan hadayun ƙonawa da sadakoki.”

34Da Yesu ya ga ya amsa da hikima, sai ya ce masa, “Ba ka da nisa da mulkin Allah.” Daga lokacin, ba wanda ya yi karambani yin masa wata tambaya.

Kiristi Ɗan Wane ne?

35Yayinda Yesu yake koyarwa a filin haikalin, sai ya yi tambaya, ya ce, “Yaya malaman dokoki suke cewa Kiristi ɗan Dawuda ne? 36Dawuda da kansa ya yi magana ta wurin Ruhu Mai Tsarki, ya ce,

“ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina:
“Zauna a hannun damana,
sai na sa abokan gābanka
a ƙarƙashin sawunka.” ’
Zab 110.1

37Dawuda da kansa ya kira shi ‘Ubangiji.’ To, ta yaya kuwa zai zama ɗansa?”

Taro mai yawa suka saurare shi da murna.

38Saʼad da Yesu yake koyarwa, ya ce, “Ku lura da malaman dokoki. Sukan so yin tafiya a manyan riguna, a kuma dinga gaishe su a wuraren kasuwanci. 39Sukan kuma nemi wuraren zama mafi daraja a majamiʼu, da kuma wuraren zaman manya a bukukuwa. 40Suna ƙwace gidajen gwauraye, kuma don nuna iyawa, sukan yi dogayen adduʼoʼi. Irin mutanen nan, za su sha hukunci mai tsanani sosai.”

Bayarwar Gwauruwa

41Yesu ya zauna ɗaura da inda ake bayarwa, ya kuma dubi yadda taron suke sa kuɗinsu a cikin baitulmalin haikali. Masu arziki da yawa suka zuba kuɗaɗe masu yawa. 42Amma wata matalauciya gwauruwa, ta zo ta saka anini biyu, da suka yi daidai da rabin kobo.

43Yesu ya kira almajiransa wurinsa, ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, abin da matalauciya gwauruwan nan ta zuba cikin baitulmalin nan ya fi na sauran dukan. 44Dukansu sun bayar ne daga cikin arzikinsu; ita kuwa, daga cikin talaucinta, ta ba kome-duk abin da take da shi na rayuwa.”

Copyright information for HauSRK